Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zubi Da Tsarin Zaben Shugaban Kasa Da Na Gwamna Duk Daya Ne


Zaben 2015: Wasu kayan aikin da akayi amfani dasu a wata mazaba a Kano
Zaben 2015: Wasu kayan aikin da akayi amfani dasu a wata mazaba a Kano

Yadda masu zabe suka yi murna a zaben shugaban kasa da yan majilisar tarayya da ya sanya hukumar zabe kara nuna ma masu kada kuriaar na iya tsayawa su saurari sakamakon zaben gwamna da ya majilisar dokokin jiha daga runfunar zaben su matukar dai hakan ba zai tada husuma ba.

Mataimakin darektan hulda da jamaa na hukumar zaben Mr Nick Dazan yayi Karin bayani.

‘’Ba abinda ya canza wajen anfani da naurar tantancewa ko anfani da katin din-din-din ko kuma wajen idan mutum ya kada kuria yana iya saurara cikin lumana kafin a sanar da sakamakon zabe a wannan cibiya duk wadannan suna nan daram dam babu wani canji da akayi musu babu wani sauyi da akayi musu’’

Masu sharhi akan lamurran yau da kullun irin su Nasiru Gambo Malumfashi na hango zaben zai iya bada mamaki.

‘’Wasu gwamnoni da suka tsaya ko kuma yan siyasa da suke da tasiri a zaben 2011 ko 2007 sun nemi takaran majilisar dattawa sun fadi wannan dama shine demokaradiyya kuma shine ci gaban demokaradiyya, ayi zabe ace anci ayi zabe acan fadi kuma aci gaba ita kuma demokaradiyyar tana kara samun gindin zama a Najeriya’’

Anasa bangare wani kwararre a harkar tsaro Mack Banite ya shawarci yan takara da suyi koyi da shugaba Jonathan wajen amincewa da sakamako, hakanan kuma wanda baiyi nasara ba to yayi koyi da janar Muhammadu Buhari da yayi takara sau 4 kafin samun nasara.

‘’Yace koda ka fadi sau daya biyu ukku kaci gaba da kokartawa har sai ka samu abinda kake so’’

Sheik Yakubu Musa Hassan Katsina na ganin ba dai-dai bane a zabi masu tabiaar bada kudi ranar zabe.

‘’Wannan ya gwada cewa wadanda suke yin wannan makiyan jamaa ne wadanda suke so sici gaba da mayar da mutane bayi ne wadanda suke kashe yayan al’umma ta basu kwaya da wewe da sauran su suna ainihin debe nasu yayan suna kaiwa turai suna karatu’’

Hakika baya ga jamiyyar PDP da APC jamiyyar APGA ta marigayi Ujukwu tana da yan takara har ma anan arewacin Najeriya, kamar tsohon ministan labaru Labaran Maku dake takara a jihar Nasarawa, da Alhaji Abdullahi Tsaure a Katsina da yace sam ba zai janye takarar sa ba, Ysiohon ministanYarima Ingama sun fidda sanarwan ci gaba da zama a PDP da mara wa yan takarar jamiyyar baya ba kamar yadda ake cewa sunbi sahun yan sauyin sheka ba.

XS
SM
MD
LG