Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zulum Na Jimamin Mutuwar Jami'an Tsaronsa 11


Gwamnan Jihar Borno, Prof. Babagana Umaru Zulum (Hoto: Twitter @ProfZulum)
Gwamnan Jihar Borno, Prof. Babagana Umaru Zulum (Hoto: Twitter @ProfZulum)

Gwamnan jihar Borno Prof. Babagana Umara Zulum ya bayyana alhininsa bisa mutuwar wasu jami’an tsaronsa 11 da suke rufawa tawagarsa baya tare da yin jinjina ga irin sadaukar da kansu da suka yi.

Prof. Zuluma ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter, bayan wani harin kwantan-bauna da wasu mahara suka kai kan ayarin motocinsa a tsakanin garin Monguno da Baga a ranar Juma’a a jihar ta Borno da ke area masa gabashin Najeriya.

"@ProfZulum na bakin cikin mutuwar jami'an tsaron da suke rufa mai baya, yana kuma yin jinjina ga sadaukar da rayuwarsu da suka yi."

Gwamnan na kan hanyarsa ne ta zuwa garin Baga a lokacin da jami’an tsaron suka gamu da ajalinsu kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter a ranar Asabar.

Jami’an sun hada da sojoji, ‘yan sanda, da kuma akalla mambobin kungiyar sintiri da ake kira Civilian JTF 2.

Gwamna Zulum ya je Baga ne domin ci gaba da shirye-shiryen maida ‘yan gudun hijira zuwa garuruwansu na asali, wadanda kungiyar Boko Haram ta raba da muhallansu tun 2014, bayan kafa kwamitin makonni biyu da suka gabata, karkashin jagorancin kwamishinan ma’aikatar shari’a na jihar Barrister Kaka Shehu Lawan.

Bisa ga majiyun harin bai hana gwamnan da tawagarsa isa Baga ba, inda suka kwana domin ci gaba da wannan shiri.

Shi dai gwamnan ya tafi Baga ne ta jirgi mai saukar angulu yayin da tawagar tasa suka tafi ta hanyar mota.

Maharan da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne, sun kai wa tawagar harin ne a kauyen Cross Kawa da ke kusa da barikin sojan hadin gwiwa da ya kunshi sojojin kasashen Chadi, Kamaru, da Nijar.

Idan ba a manta ba, kwanaki hudu da suka gabata, aka kai wa jami’an sojoji hari a Damboa aka kashe babban kwamandan soja na garin Kanar Dahiru Bako.

Wannan ne karo na biyu da ake kai wa tawagar gwamnan hari cikin shekara guda.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG