Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janar Tukur Yusuf Buratai Ya Jinjinawa Marigayi Kanar Bako


Janar Tukur Buratai

Wuni guda bayan jana’izar Kanar Bako, babban hafsan sojojin Najeriya ya jinjinawa kwmandan soji Kanar DC Bako da Mayakan kungiyar Boko Haram suka kashe

Rahotanni sun yi nuni da cewa, babban jami’in sojin ya rasu ne a ranar Litinin a wani harin kwantan bauna da 'yan ta'addan suka yi musu.

Kafn kashe shi, Kanar Bako shine kwanmanda na rundunar Operation Lafiya Dole, wani rukunin zaratan sojoji masu yaki da ayyukan ‘yan ta’adda a yakin arewa maso gabashin kasa.

Da yake tabbatar da labarin, mai magana da yawun rundunar Operation Lafiya Dole, Ado Isa, ya ce kwamandan sojin ya rasu ne a asibitin sojoji inda ake duban kafiyar sa biyo bayan harin kwantan bauna da aka kai masa.

Babban hafasan hafsoshin sojojin Najeriya, laftana Janar Yusuf Tukur Buratai ya kwatanta mutuwar marigayin da fadiwar babban bango a gidan soja. Ya fada ta bakin mai magana da yawun sa Sagir Musa, cewa, Kanar Bako hazikin ma’aikaci ne mai kula da jarumtaka a wurin gudanar da aikin sa.

Ganin irin rawar gani da Kanar Bako ya taka wurin kare birnin Damaturu daga hare haren Boko Haram lokacin da yake kwamanda a cikin birnin, gwamnati da mutane jihar Yobe sun yi zaman makokin na jarumin sojan.

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, ya bayyana Kanar Bako a matsayin jajirtaccen jarumin soja da ya sadaukar da rayuwar sa domin kare Najeriya da ‘yan Najeriya. Ya kuma bayyana alhinin sag a wannan babban rashi.

Daya daga cikin mutane da marigayin ya ceci rayuwar su, ta zanta da sashen Hausa, inda ta bayyana cewa, Kanar Bako ya ceci ta a lokacin da ‘yan Boko Haram suka kai hari a asibitin Maryam Abacha dake kan hanyar Gashua a Damaturu, inda taje haifuwa.

Gai rahoton Hassan Maina Kaina daga birnin tarayya Abuja:

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

Facebook Forum

Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG