Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zulum Ya Ce Harin Da Aka Kai Kan Tawagarsa Zagon Kasa Ne


Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum
Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana tababa a kan harin da aka kai tawagar motocinsa a garin Baga, lokacin wata ziyara da ya kai a garin.

Ya ce "wannan al'amari ba na rashin isassun ma’aikata ba ne, ba kuma rashin kayan aiki, bane. Abin da ya faru a Baga zagon ƙasa ne kawai tsagoransa, don haka kar mutane su ƙalubalanci Shugaban Ƙasa, ko wani Buratai."

Ya kara da cewa "amma duk da haka ya kamata a sake duba yadda ake bada umarni dangane da wannan aikin." Gwamnan ya ce wannan hari dai ba zai sa shi ya karaya ba,

A cewarsa “jiya mun zo nan garin Kukawa, Baga kwana uku da ya shige, mutane sun kai kamar dubu ɗari biyar a nan garin, alal haƙiƙa mun baiwa mutane sun kai dubu tamanin abinci, sauran yaransu ne.

"Ba yadda za'a yi gwamnati, ko wata Ƙungiyar agaji su zo su ba da abinci ga mutane ɗari biyar. Abunda muke so ba wani abu bane, mutane su koma garinsu, musamman Baga."

Bayan harin na Baga, an kuma kai wani hari a kan wata tawagar da ke sharewa gwamnan hanya da ake kira Advance Party, a cewar ɗaya daga cikin abokan gwamnan da ake kira Injiya Bakinzare wanda ya sha da ƙyar.

Rundunar ‘Yansandan Jihar Borno ta bakin Mataimakin Kakakinta ASP Yakubu Mohammed, ta ce suna sane da harin sai dai ba su da cikakken rahoto a kai. Amma a cikin rahotannin da suka samu ba bu kisa, kuma har yanzu suna tattara bayanai kan harin

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG