Dan Takarar Gwamna A Tutar Jam’iyyar APC Ya Tsallake Rijiya Da Baya

INEC

Hukumar INEC tace 'yan bindiga sun sace mata wasu ma’aikata kuma har yanzu ba’a gane suba

An shiga wani sabon yanayi a zaben ‘yan majalisun jiha dana tarayya a jihar Rivers, da hukumar zaben mai zaman kanta ke kokarin kammalawa tun ranar asabar din data gabata.

Maganan da ake yi yanzu shine cewar hukumar zabe mai zaman kanta a jihar ta Rivers, ta fitar da sanarwa cewar ta dakatar da komai dangane da zaben har sai abinda hali yayi a sakamakon yadda ake ta kashe kashe na tashin hankali masamman tsakanin jam’iyyar PDP, da APC, dake adawa da juna.

Hukumar ta INEC, dai ta nuna cewa ‘yan bindiga sun sace mata wasu ma’aikata kuma har yanzu ba’a gane suba, hukumar da INEC, tace ta soke zabubbukan kananan hukumomi takwas daga cikin wadanda ake sake zabe,an dai yi kashe kashe da dama a wannan zaben.

Mataimakin babban Sefeto janar na ‘yan Sandan Najeriya, Baba Adisa Bolanta, mai kula da shiya ta shida kuma shugaban gamayyar tsaro a wannan zaben yace an samu salwantar rayuka awannan zaben saida bai kai yadda ake ta fadi ba, kuma wandanda suka mutu an kashe sune a wurare daban daban tsakanin daren jiya da safiyar yau litinin an samu harbe harbe a wasu unguwani a cikin birnin Fatakol.

Dan takarar Gwamna a tutar jam’iyyar APC, Dr. Dokuku Peterside, ya tsallake rijiya da baya a lokacin da ‘yanbindiga suka afkamasa.