Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu zanga-zanga sun tsare hanya a kamfen din Trump na Arizona


Dan Takarar Jam'iyyar Republican, Donald Truimp
Dan Takarar Jam'iyyar Republican, Donald Truimp

Dan takarar shugabancin Amurka na sahun gaba a jam’iyyar Republican Donald Trump, yana zagayen yakin neman zabe a dausayin Fountain Hills na jihar Arizona kusa da kan iyakar Amurka da Mexico.

Yana kuma tare da ‘yan jam’iyyarsa da ke garin kamar su Sheriff Joe Arpaio da kuma tsohowar gwamnar jihar ta 22 wato Jan Brewer, inda kuma a bainar jama’a suka marawa Trump baya game da cewa shine dan takararsu.

Kaso 30 dai na jama’ar jihar Arizona ‘yan kabilar Latino ne, sannan daya daga cikin manyan jihohin da dan takarar zai so lashe zaben fidda gwani a cikinta a zaben da za a yi a ranar Talata mai zuwa.

Masu zanga-zangar kin jinin Trump dai sun yi sammakon tare babbar hanyar zuwa unguwar Phoenix da ke da dimbin jama’a.

Inda masu zanga-zangar suka gindaya motocinsu kamar guda 50 a tsakiyar hanyar, suna kuma dauke da kwalayen da ke cewa, ‘Trump Shirme Ne’.

XS
SM
MD
LG