Isra’ila Ta Kara Yawan Ministocin A Gwamnatin Hadin Guiwa

Ntanyahu

Amma nadin wani mutum mai ra’ayin rikau a matsayin dan majalisar ministocin kasar ya janyo suka

Firayin ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya kara yawan ministocinsa dake cikin gwamnatin shi ta hadin guiwa, amma nadin wani mutum mai ra’ayin rikau a matsayin dan majalisar ministocin kasar ya janyo suka, daga cikin kasar da ma wajen ta.
Netanyahu ya rattaba hannu a yarjejeniyyar hadin guywar ne a Knesset, majalissar Isra’ila, tare da sabon ministan nashi da aka yi ta takaddama a kansa, Avigdor Lieberman, wanda ke ya shugabantar jam’iyyar Yisrael Beitenu.
Liberman yana daya daga cikin mutanen da suka yi kaurin suna saboda irin lafazin batanci da yake anfani da shi a jawabansa kuma yana da ra’ayin rikau sosai game da Paladinawa. Zai yi aiki a matsayin sabon ministan tsaron kasar, inda zai taka muhimmiyar rawa wajen fidda muhimman manufofin kasar akan tsaro, yaki da zaman lafiya.