Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Tabbacin Mutuwar Shugaban Boko Haram- Kanar Kuka Sheka


Abubakar Shekau da mayakan Boko Haram
Abubakar Shekau da mayakan Boko Haram

A firar da ya yi da Muryar Amurka kakakin sojin Najeriya Kanar Sani Kuka Sheka yace su sojoji basu tabbatarwa kowa ba mutuwar shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau.

Yayinda yake bada bayani yace su 'yan Boko Haram dake cikin dajin Sambisa suna da rarrabuwar kawuna saboda barin wuta da sojoji ke yi masu.

Misali ranar Litinin wani bala'i ya auka masu. Babban jami'i dake hada masu bam ya nemi ya gudu da ya ga uwar bari sai wani dake tsare lafiyar shugaban nasu ya dauki bindiga ya harbeshi. Wanda kuma ya maye gurbinsa a kokarin hada bam da shi ma yake yi ya samu hadarin da ya makantar dashi.

Akan ko wanene shugaban Boko Haram Kanar Kuka Sheka yace kowa ya sani Abubakar Shekau ne, kenan rahoton da aka bayar can baya kamar babu kanshin gaskiya a ciki. Kanar Kuka Sheka ya kara da cewa su sojoji basu fada tabbas ba cewa shugaban Boko Haram ya mutu.Yace idan suna da tabbacin haka zasu fada.

Dangane da 'yan matan Chibok da ake kyautata zaton har yanzu suna dajin Kanar Sheka yace suna zaton hakan, shi ya sa suka fito da shirin kewaye dajin saboda manufofi biyu. Manufar farko itace a kakkabe 'yan Boko Haram kana ta biyu itace duk mutanen da 'yan ta'adan ke rike dasu a dajin su samu su kubutar dasu.

Duk inda 'yan ta'adan suke sojoji zasu yi kokarin kawar dasu. Ya kira jama'a su dinga taimakawa da labari, musamman idan sun ga wanda ba idon sani ba ne saboda 'yan ta'adan suna neman sulalewa domin sun ga uwar bari.

Ga cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:10:16 0:00

XS
SM
MD
LG