An Bukaci Britaniya Tayi Saurin Ficewa

Kasashen turai sun maida hankali akan makomar kungiyar ba tare da kasar Britaniya ba

Yau Laraba shugabanin kungiyar kasashen turai sun maida hankali akan makomar kungiyar ba tare da kasar Britaniya ba. Shugabanin suna duba makomar kungiyar a yayinda suke kamalla taron koli a birnin Brussells kasar Belgium, kwanaki bayan turawan Ingila sun jefa kuri’ar ficewa daga cikin kungiyar.

Shugabanin kungiyar sun bukaci kasar Britaniya data yi saurin ficewa daga cikin kungiyar, kada kuma ta zaci zata samu moriyar ko kuma alfanun kungiyar ba tare da biyan komai ba.

Tana yiwuwa wannan ne taron koli na karshe da Prime Ministan Ingila David Cameroon zai halarta a matsayin sa na Prime Minista. Domin kuwa zai yi murabus daga mukamin nasa bayan gwamnatin sa ta kasa shawo kan yan kasar sa, da su yi zabin ci gaba da kasancewa cikin kungiyar kasashen turai.