Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matar Shugaban Amurka Ta Kai Ziyara Makarantar 'Ya'ya Mata A Liberiya


Matar Shugaban Amurka Michelle Obama

Matar Shugaban Amurka Michelle Obama, ta kai ziyara sansanin koyar da 'ya'ya mata shugabanci a kasar Liberiya jiya Litini, wanda hakan wani bangare ne na jaddada ilimin 'ya'ya mata a Afirka.

Michelle Obama ta gana da mata matasa a Kakata, inda ake gudanar da shirin samar da ma'aikatan wanzar da zaman lafiya, bayan da aka yi mata tarba mai kyau, ciki har da raye-rayen gargajiya, a babban birnin kasar Monrovia.

Tun farko a jiya din, ta gana da Shugabar Liberia Ellen Johnson Sirleaf, mace ta farko da aka zaba Shugabar kasa a Afirka.

Matar Shugaban Amurka din na tafiya ne da 'ya'yanta mata - wato Malia 'yar shekaru 18 wacce ta kammala makarantar sakandare wannan shekarar, da kuma Sasha 'yar shekaru 15, da kuma kakarsu, Marian Robinson.

Ziyarar tasu ta tsawon kwanaki 6 ta hada da yada zango a Morocco da Spain, kuma za ta jaddada shirin, "A Bar 'ya'ya Mata Su Ilimantu" wanda wani babban shiri ne da Michelle Obama ta bullo da shi. Shirin ya kunshi kawar da matsalolin da su ka hada da auren dole da fatara da kuma tashe-tashen hankula -- wadanda duk ke hana 'ya'ya mata kimanin miliyan 62 a fadin duniya kasancewa a makaranta.

XS
SM
MD
LG