DOMIN IYALI: Yadda Matan Najeriya Zasu Tinkari Zaben 2023-Kashi Na Hudu, Satumba,01, 2022

Alheri Grace Abdu

Yau ma muna tare da Hajiya Khadija Abdullahi Iya ‘yan takarar gwamnan jihar Naija ta jam’iyar AFGA, da Mrs Dorathy Nuhu Aken ‘Ova wadda ta nemi a tsaida ita takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyar SDP, sai kuma Hajiya Mariya Ibrahim Baba ‘yar siyasa kuma ‘yar gwaggwarmaya, da kuma dan siyasa Sa’idu Gombe, wadanda ke musayar miyau kan matakan da mata za su iya dauka domin ganin an dama da su a fannin siyasa da harkokin mulkin Najeriya.

A yau bakin sun yi muhawara kan abinda ke kawo koma bayan siyasar mata.

Saurari cikakken shirin da Shamsiya Hamza Ibrahim ta jagoranta: