A BARI YA HUCE: Labarin Mai Santin Rake Da Mai Santin Shinkafa, Afrilu, 10, 2021

Alheri Grace Abdu

A wannan makon bakon shirin A Bari Ya Huce, dan jarida Ado Hazzad ya bada labarai biyu na gwanayen santi.

Mutum na farko ana bude baki bara, bayan ya yi laumar shinkafa sai ya daga kai yace, "shin nawa ake saida buhun siminta a shekara ta dubu dari tara da tamanin?" sai abokan su ka ce "ko dai nawa a ke sayar da buhun shinkafa?"

Na biyu kuma yana shan rake lokacin da kotu ta soke zaben gwamnan jihar Anambra Chris Ngige sai ya ce "wai tsohon gwamnan jihar Anambran da aka tsige ina zai tafi yanzu?" sai abokan suka ce "ba sai ya tafi Makarfi ba ya yi noman rake?"

Saurari cikakken shirin:

Your browser doesn’t support HTML5

A Bari Ya Huce: Labarin Mai Santin Rake Da Mai Santin Shinkafa 24: 00"