A BARI YA HUCE: Labarin Miji Mai Satar Cincin- Yuni,05, 2021

Alheri Grace Abdu

A wannan shirin mun bada labarin wata mace mai sana'ar cincin sai ta lura kullum idan ta tashi sai taga cincin din ya ragu kuma ta sayar babu riba. Sai wata rana ta yanke shawara ta zauna cikin dare ta ga ko bera ne ya ke yi mata barna. Tana zaune cikin duhu sai ta ji ana tauna Kurmus Kurmus, ta yi sauri ta haska fitila sai ta ga ashe mijinta ne ke lallabowa ya ci cincin cikin dare. Da dai su ka hada ido sai yace "na ci cincin na Hamsim".

Saurari cikakken shirin:

Your browser doesn’t support HTML5

A Bari Ya Huce:Labarin Miji Mai Satar Cincin 24: 00"