Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A BARI YA HUCE: Labarin Ango Mai Fitsarin Kwance Afrilu, 24, 2021


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

A wannan shirin mun bada labarin wani saurayi da aka yiwa aure ashe yana fitsarin kwance amarya bata sani ba daren farko ango ya tafka fitsarin kwance akan gado amarya ba ta sani ba. Ya rasa yadda zai yi ga gado duk ya jike, sai ya yi hikima ya tada amaryar daga barci ya tambayeta "idan kika yi mafarki Zaki da Kura sun biyo ki yaya za ki yi? Sai Amarya tace hmm tabdijam ai wallahi sai na yi Tutu da fitsari don tsoro idan na yi wannan mugun mafarkin. Sai ango yace hmm!, ashe dai na yi ta maza tunda ni fitsari kawai na yi".Sai amarya ta taba gado taji a jike, tace ai kuwa babu shakka ka nuna bajimta. Ai da ni ce wallahi sai na yi tutu.

A Bari Ya Huce: Labarin Ango Mai Fitsarin Kwance24: 00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:24:35 0:00  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG