A Fara Duba Watan Ramadan Daga Jumma’ar Nan- Majalisar Koli Ta Musulunci

Hoton jinjirin Wata

Majalisar koli ta musulunci a Najeriya ta bukaci musulmi su fara duba watan ramadan na bana hijira 1443 daga jumma’ar nan.

Sanarwar daga majalisar da ke karskashin jagorancin sarkin musulmi Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar ta ware lambobin waya da adireshin wasika na yanar gizo don isar da sanarwar wanda ya ga watan.

Hakan na zuwa ne yayin da musulmai a fadin duniya ke ci gaba da shirye-shiryen fara Azumin Ramadan na shekara-shekara.

Idan an samu ganin watan daga daren jumma’ar to za a tashi da azumin ranar asabar.

A tsarin bisa ka’idar shari’ar Islama, in ba a ga watan ba, a jumma’a da ta ke daidai da 29 ga watan Sha’aban, za a tashi da azumi ranar lahadi 3 ga watan Afrilu.

An samu nasarar raguwar rabuwar kawunna daga wadanda ba sa daukar azumi ko ajiye wa a kan lalle sai sun ga watan da idon su.