Abba Gida-Gida Ya Ba Abba Al Mustapha Mukami A Kwamitin Karbar Mulki

Abba Al Mustapha (Instagram/Abba El Mustapha)

"Ina kara godiya ga zababben Gwamna mai jiran gado na jihar Kano, Eng. Abba Kabir Yusuf bisa wannan dama da ya ba ni.” Al Mustapha ya rubuta shafinsa na Instagram.

Zababben gwamnan jihar Kano a Najeriya, Abba Kabir Yusuf, ya nada fitaccen jarumin masana’antar Kannywood Abba Al Mustapha a matsayin Sakataren kwamitin nishadi.

Al Mustapha ne bayyana hakan a shafinsa na Instagram a ranar Juma’a inda ya wallafa hotonsa da lokacin da aka ba shi takardar nadin mukamin.

"Ina kara godiya ga zababben Gwamna mai jiran gado na jihar Kano, Eng. Abba Kabir Yusuf bisa wannan dama da ya ba ni.” Al Mustapha ya rubuta shafinsa nasa.

Tuni abokan sana’arsa da masoyansa suka yi ta aike masa da sakon taya murna.

“Masha Allah. Congrats Yaya Abba. Allah ya sa a dace.” In ji Jarumi Baballe Hayatu.

“Masha Allah. Congratulations Yaya Abba.” In ji Bashir Mai Shadda.

“Ma Sha Allah. Congratulations Allah ya yi jagora. Ameen.” Sidi Ishaq ya ce.

“Congratulations.” In ji jaruma Saratu Daso.