Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Furodusa Bashir Maishadda Zai Auri Jaruma Hassana Muhammad


Furodusa Maishadda, hagu da jaruma Hassana Muhammad, dama (Instagram/ Bashir Maishadda/ Faisal Photos/ Hassana Muhammad/ Bala Photos)
Furodusa Maishadda, hagu da jaruma Hassana Muhammad, dama (Instagram/ Bashir Maishadda/ Faisal Photos/ Hassana Muhammad/ Bala Photos)

Jaruma Hassana Muhammadu na daya daga cikin jaruman Kanyywood mata da tauraronsu ya haska musamman a shekarar 2020.

Furodusa a masana’antar Kannywood da ke arewacin Najeriya Bashir Abdulkareem Mai Shadda, zai angwance da amaryarsa jaruma Hassana Muhammad.

Za a daura auren ne a unguwar Masallacin Murtala da ke Kano a ranar 13 ga watan Maris kamar yadda Maishadda ya sanar.

“Ina farin cikin gayyatar masoya daurin aurena. Wadanda kuma ba za su samu damar zuwa ba, sai a taya mu da addu’a.” Mai Shadda ya rubuta a shafinsa na Instagram hade da katin gayyata a ranar Talata.

Jaruma Hassana Muhammadu na daya daga cikin jaruman Kanyywood mata da tauraronsu ya haska musamman a shekarar 2020.

Ta fito a manyan fina-finai irinsu “Hafiz” da “Hauwa Kulu,” tare da Umar M. Shareef, wadanda duk kamfanin Maishadda Global Resources ne ya shirya.

Kazalika ta fito a fim din Mujadala da aka sabunta. Sai dai an dena jin duriyarta a baya-bayan nan a fina-finan na Kannywood.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG