Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Sahabi’ Ya Samu Karuwa Da Da Namiji


Jarumi Ali Hussein, wanda aka fi sani da Sahabi a shirin Kwana Casa'in mai dogon zango

“Allah ya raya #Ramadan, Alhamdulillahi, yaro ina maka maraba da zuwa duniya.” In ji jarumi Ali Hussein.

Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood a arewacin Najeriya, Ali Hussein, wanda aka fi sani da Sahabi a shirin Kwana Casa'in na Arewa 24, ya samu karuwa da da namiji.

Jarumin ne ya wallafa labarin a shafinsa na Instagram yana mai nunawa godiyarsa ga Allah.

“Allah ya azurta ni da samun da namiji.” Tuni dai har ya radawa dan suna.

“Allah ya raya #Ramadan, Alhamdulillahi, yaro ina maka maraba da zuwa duniya.” In ji jarumi Hussein, wanda ke fitowa a shirin na Kwana Casa'in mai dogon zango a matsayin dan jarida.

An dai ga jarumin ya wallafa wani dan takaitaccen bidiyon jaririn wanda aka rangadawa ado.

Shi kuma a daya gefen ya saka tufafi na Larabawa yana murmushi har da saka tabarau - wani abu da ke nuna yana cikin yanai na farin ciki.

Tuni abokanan sana’ar jarumin da masoyansa suka yi ta tururuwar taya shi murna.

“Allah ya raya” In ji jaruma Saratu Doso.

“Allah ya raya Ramadan.” Umar Abdullahi ya ce.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG