Adamawa: Ana Cece-kuce Game Da Karbo Bashi

Mazauna kauyukan Adamawa na tserewa daga Boko Haram.

A Jahar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, an fara ta da jijiyar wuya game da basussuka da ake zargin sabuwar gwamnatin gwamna Sanata Muhammadu Ummaru Jibrilla Bindo ke karba domin gudanar da wasu hidimomin jahar.

Wasu masu fashin baki sun ce yawan karbar bashin zai iya karya tattalin arzikin jahar musamman idan ba a amfani da kudaden ta hanyoyin da suka dace.

“Bashi na da dadin karba, biya ne matsala, yawancin basussukan za ka ka ji ana cewa za a biya su nan da shekaru 20 wani kuma goma, al’umar da ke gaba za su iya shiga matsala, gwamnati ya kamata ta zauna ta yi nazari.” A cewar Barrister Sunday Joshua, masani a fannin sarrafa kudaden gwamnati.

Ita ma dai dai jam’iyyar adawa ta SDP, ta koka da yadda ake zargin gwamnatin ta Bindo da karbo basukan.

“Na kasa gane yanayin wannan gwamnati, ka zo ka tarar ana bin ka basussuka, baka biyaba ka fara cin wasu basussukan, mun zauna ke nan a kan biyan basussuka babu ci gaba ke nan?” In ji shugaban jam’iyyar, Malam Ibrahim Bebeto.

Ya kuma kara da cewa abin takaicin shi ne ana cin bashin ne domin a biya kudaden albashi ba wai ana amfani da su ne ba wajen bunkasa jahar ba.

Sai dai gwamnan Jahar Bindo ya musanta rade-raden da ake yi na cewa ya ciyo bashin makudan kudade, yana mai cewa biliyan tara kawai suka karba daga bankin tarayya domin biyan ma’aikata hakkokinsu.

“Biliyan tara aka bayar kuma za a biya a cikin shekara 20, kuma bashin nan da muka samu hakkin talaka da gwamnatin ‘yan adawa suka yi shekara 16 ba su biya ba ne, idan wani ya ce maka biliyan 19 ne karya ne.” In ji Bindo.

Domin jin karin bayani saurari wannan rahoto da wakilin Muryar4 Amurka Sanusi Adsamu ya hada:

Your browser doesn’t support HTML5

Adamawa: Ana Cece-kuce Game Da Karbo Bashi- 2’13”