Al'ummomi Sun Kosa Kan Batun Yaki Da Boko Haram A Nijar

Shugaba Buhari Da Takwaransa Na Nijar a Taron Kungiyar Tarayyar Turai

Al’umomi a Jamhuriyar Nijar suna kira ga hukumomi su dauki matakin magance matsalolin Boko Haram da suke kara zafafa kai hare hare da aikata wasu miyagun ayyuka a ‘yan kawanakin nan a yankin Diffa inda satar mata da yara kanana domin neman kudin fansa ke kokarin samun gindin zama.

Lamari na baya bayan nan shine wanda ya faru a wasu kauyukan da’irar Tomourour inda ‘yan bindiga suka sace ‘yan mata 15, kwanaki 500 bayan sace rukunin farko mai kunshe da mata da yara kanana kimanin 39 a kauyen Ngalewa abinda ‘yan majalisar dokoki daga mazabar wannan yanki suka yi tur da shi

Kungiyoyin kare hakkin mata sun bayyana kaduwa da yadda wannan al’amari ke kara tsananta duk kuwa da cewa doka ta haramta cin zarafin dan adam a Nijer.

Matsalolin ta’addanci a Jamhuriyar Nijer wani abu ne da ya mayar da dubban yara marayu wadanda aka hallaka iyayensu a filin daga ko wadanda aka tarar a cikin gida.

Rahotannin yammacin litinin 26 ga watan Nowamba na cewa, biyu daga cikin ‘yan matan da aka sace a daren juma’a 23 ga wata sun yi nasarar tserewa daga hannun ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da su.

Zaman dar dar din da aka shiga a yankunan da kungiyoyin ta’addanci ke cin karansu ba babbaka ya sa wasu iyaye a karkara soma dari darin sanya ‘yayansu aikace aikacen da a can baya yara musamman ‘yan mata ke yi domin walwalar iyali .

Saurari karin bayani a kan wannan batu a shirin Domin Iyali ranar alhamis