Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Hari Da Aka Kai Yayi Sanadiyyar Mutuwar Ma'aikata A Niger


Wasu 'Yan Kungiyar Boko Haram Sunyi Sanadiyyar Mutuwar Ma'aitan Kamfanin Faraco A Kauyen Toumour Dake Jamhuriyyar Niger.

A jamhuriyar Nijer wasu ‘yan bindigar da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun hallaka wasu ma’ikatan kamfanin Foraco mai aiyukan gina famfunan karkara, yayinda wasu suka ji rauni a sakamakon harin da suka kai a jiya da daddare a kauyen Toumour a yankin Diffa.

Bayanai daga mazaunan kauyen Toumour, na cewa da misalin karfe 2 na daren jiya Laraba, wayewar yau Alhamis ne wasu ‘yan bindigar da suka shigo gari akan dawakai, inda suka budewa jami’an kamfanin Foraco wuta, wadanda ke yada zango a ma’aikatar magajin gari, akan hanyarsu ta zuwa karkarar Bosso domin aiyukan gina fanfuna.

Magajin garin Toumour Alhaji Mani Orte, yayi ma shashen Huasa na Muryar Amurka bayanin, inda ya tabbatar da faruwar wannan al’amarin. Kauyen Toumour mai yawan al’uma kusan 13,000 nada nisan kimanin kilomita 80, daga gabacin Diffa babban birnin jihar, yayinda ta bangaren kudu garin ke da nisan kilomita 7 da iyaka da jihar Borno a Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG