Amurka Zata Rufe Ofisoshin jakadancinta 21 Gobe Lahadi

Jerin kasashen da Amurka zata rufe ofisoshin jakadancinta ranar lahadi 4 Agusta, 2013 saboda barazanar tsaro

Gwamnatin Amurka ta gargadi Amurkawa da su yi hattara sosai lokacin tafiye-tafiye a kasashen duniya, saboda barazanar hari daga al-Qa’ida.
Gwamnatin Amurka ta gargadi Amurkawa da su yi hattara sosai lokacin tafiye-tafiye a kasashen duniya, tana mai gargadi musamman game da barazanar harin ta’addanci daga al-Qa’ida.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fada jiya jumma’a cewa yiwuwar fuskantar ta’addancin ta fi karfi a Gabas ta Tsakiya da Afirka ta Arewa. Ta ce ana iya fuskantar farmaki daga yankin Arabiya.

Sanarwar ta kara da cewa al-Qa’ida da kawayenta su na iya kai hare-hare kowane lokaci daga yanzu har zuwa karshen watan Agusta.

Wannan jan kunne yana da nasaba da bayanin leken asirin da ya sanya Amurka zata rufe ofisoshin jakadanci 21 gobe lahadi a kasashe dabam-dabam, akasarinsu kasashen Musulmi.

Har ila yau a jiya jumma’a, Britaniya ta ce zata rufe ofishin jakadancinta dake Yemen gobe lahadi da jibi litinin a saboda batutuwan tsaro da suka taso. Ta ce musamman ta damu da sha’anin tsaron a ranakun karshe na azumin watan ramadan.