An Baiwa Tsaffin Mukarraban Trump Umarnin Bada Ba'asi Akan Alaka Da Rasha

Trump da Putin

Ana kokarin jin gaskiyar alaka mukarraban shugaba Donald Trump da kasar Rasha

Kwamitin Majalisar dattijan Amurka, da yake binciken zarge zargen cewa Rasha tayi shishigi a zaben shugaban Amurka, ya baiwa tsaffin mukarraban shugaba Donald Trump umarnin su bada duk wani bayani da suke dasu na yiwuwar wata alaka da yan Rasha.

Haka kuma kwamitin ya bukaci bayanai daga tsohon shugaban yakin neman zaben shugaba Trump Paul Manafort da mai bashi shawara Roger Stone da kuma mai bashi shawara akan matakan tsaron cikin gida Micheal Flynn a zaman wani bangare na binciken.

Kwamitocin Majalisar dattijai dana wakilai tare da jami’an hukumar binciken aikata laifuffuka ta FBI duk suna binciken yunkurin Rasha na yin shishigi a zaben shugaban kasar da aka yi bara anan Amirka.