Matsalar cin hanci da karbar rashawa, da ingiza farashin kaya domin cin bakar riba, da badda sawun kudaden haram, da kin biyan kudin haraji a kan lokaci, na daga cikin abubuwan da yanzu ke addabar Nigeria.
WASHINGTON, DC —
Jami’an dake gudanar da binciken halin zaman al’umma dake aiki tare da Bankin ayyukan ci gaban kasa da na al’umma a Afirka, sun bayyana cewar kasashen Afirka sun yi asasar kusan Dala miliyan dubu sau dubu uku da miliyan dari hudu ($1.4Trillion) saboda matsalar cin hanci da karbar rashawa cikin shekaru Talatin da suka gabata. Kuma mafi yawan asarar kudaden anyi ne a dalilin cin hanci da karbar rashawa da yin sama da fadin da ‘yan kasuwa keyi, da hakan kuma ke janyo koma bayan ayyukan ci gaban kasa da na al’umma a jihohin Nigeria. Ana kuma iya cewa irin arziki da kudaden dake fita daga nahiyar Afirka a dalilin cin hanci da karbar rashawa su ne ke hana ayyukan ci gaban kasa.Zancen nan da ake yi irin wadancan kudaden da aka bayyana sun nunka har sau biyu a cikin shekaru da dama da suka gabata.