Accessibility links

Kungiyar Boko Haram ta Hallaka Dubban Mutane Cikin Shekar Hudu


Shugabannin Boko Haram

Duk da kafa dokar ta baci da kara yawan dakarun soji a arewa maso gabashin Najeriya domin shawo kan kungiyar Boko Haram amma ta'adanci sai karuwa yake yi a shiyar

Kafin karshen shekarar 2013 an sha alwashin za’a shawo kan kungiyar Boko Haram mai neman kafa mulkin Islama bisa ga nata fahimtar wadda ta kwashi shekaru hudu tana yiwa arewacin Najeriya barazana da ayyukan ta’adanci. Dubun dubatan sojoji da wasu jami’an tsaro aka tura zuwa jihohi uku dake fama da ‘yan kungiyar tare da kafa dokar ta baci amma duk da haka ana cigaba da tashin hankali da yawan asarar rayuka.

Amma a watan Mayu shugaban kasar Goodluck Jonathan yace tashin hankali sai karuwa yake yi a yankin. Boko Haram ta cafke wasu sassa. Hare-haren da kungiyar ke kaiwa da kashe mutane da yin garkuwa da wasu tamkar sheilar yaki ne. Ta dalilin haka ya sa shugaba Jonathan ya kafa dokar tabaci a jihohin Borno da Yobe da Adamawa ya kuma shawarci hafsan hasoshin soji ya kara tura dakaru a jihohin.
Watanni shida na aiwata dokar ta bacin da fafatawa da sojoji suka yi da ‘yan kungiyar Boko Haram ta taimaka sun kawo zaman lafiya a birane amma ba a kauyuka da karkara ba.

Mai magana da yawun sojoji Kanal Muhammed Dole ya gayawa kafofin labarai cewa sun yanke hanyoyin da kungiyar ke samun kayan aiki. Yace “Mun samu nasarar hanasu samun kayan aiki da abinci don haka hare-haren da suke kaiwa kauyuka na neman rayuwa da rage kuncin da suke ciki ne. Basu da abinci. Basu da ruwa” in ji Dole wanda ya kara da cewa “na yi imani wasu ‘yan ta’adan sun tsallake zuwa cikin kasashe dake makwaftaka da mu”

A watan Nuwamba Amurka ta ayyana kungiyar Boko Haram da kungiyar Ansaru a matsayin kungiyoyin ‘yan ta’ada na kasa da kasa. Daga bisani gwamnatin Najeriya ta kara wa’adin dokar ta bacin da wata shida.

Kodayake an samu tsaiko na dan wani lokaci kamar yadda Dauda Tatally mai sayar da kayan naura mai kwakwalwa ya shaida amma watan Disamba ya kawar da duk wani tunanin zaman lafiya a Maiduguri yayin da kungiyar Boko Haram ta kai munanan hare-hare kan sanssanonin sojin mayakan sama da na ‘yansanda.
Sojoji sun mayar da martani da kafa dokar hana fita na sa’o’i 24 karo na farko a Maiduguri a cikin ‘yan shekarun nan. Hare-haren kwana kwanan nan sun yi sanadiyar yin rugu-rugu da da barikokin mayakan sama da na ‘yansanda. An kone motoci da jiragen sama da dimbin kayan aiki lamarin da ya sa mahukunta suka hana ‘yan jarida shiga wuraren. An yi asarar rayuka da dama.

Human Rights Watch ta ce Boko Haram ta kashe dubban mutane cikin shekaru hudun da suka gabata yayin da irin matakai masu tsanani da dakarun tsaro suke dauka na mayar da martani sun hallaka daruruwan mutane.
Wani mai bincike Eric Guttschuss yace tashin hankali tsakanin al’ummomi ya kashe mutane da yawa cikin shekaru hudun kuma gazawar gwamnati ta hukunta wadanda suka yi aika-aikar ya karfafa kungiyar Boko Haram.

Hujjar da wasu ke bayarwa dangane da rikicin kabilanci da na addini shi ne kashe Musulmai a jihar Filato amma gwamnati ta yi kunnen shegu ta kuma kawar da kanta.

Ana harsashen za’a samu barkewar rikicin kabilanci da na addini shekara mai zuwa kafin zaben kasar na shekarar 2015. Sai dai rundunar sojin kasar ta ce a shirye take yayin da take cigaba da kashe mayakan Boko Haram idan sun kai samame.

To sai dai a cikin karkara ana cigaba da kashe mutane da kone gidajensu lamarin da ya sa suna zama cikin zullumi kodayaushe.
XS
SM
MD
LG