Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya ta Ce An Kashe Mutane Fiye da Dubu Daya da Dari Biyu Tun Watan Mayu


Wannan shi ne adadin farko da wata kafa mai zaman kanta ta bayar tun kafa dokar-ta-baci a jihohin Adamawa, Borno da Yobe.

Hare-haren kungiyar Boko Haram sun haddasa mutuwar mutane fiye da dubu daya da dari biyu a yankin arewa maso gabashin Najeriya, tun lokacin da gwamnatin kasar ta ayyana dokar-ta-baci a watan Mayu.

A ranar 14 ga watan Mayu ne shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya kafa dokar-ta-baci a jihohin Adamawa, Borno da Yobe dake arewa maso gabashin kasar, a wani yunkuri na murkushe yamutsin da ‘yan Boko Haram suka haddasa.

Wannan adadin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayar, shi ne alkalami na farko da wata kafa mai zaman kanta ta taba bayarwa game da mace-macen da aka fuskanta tun lokacin da sojoji suka fara kai farmaki kan ‘yan Boko Haram a yankin.

Ofishin kula da ayyukan jinkai na majalisar ya fada cewa an kasha mutane 1,224 a hare-hare masu alaka da kungiyar Boko Haram tun daga watan Mayu.

Wannan adadi na wadanda aka kasha ya hada da fararen hula, da sojoji da kuma su kansu ‘yan Boko Haram da sojoji suka kasha a lokacin da suke kokarin fatattakar hare-haren da tsageran suka kai.

Sai dai kuma mai magana da yawun ofishin kula da ayyukan jinkai na majalisar dinkin duniya, Choice Okoro, ta fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa wannan adadin wadanda aka kasha bai hada da na ‘yan Boko Haram da suka mutu a hare-haren da sojoji suke shiryawa suke kuma kaiwa kan sansanonin sub a.

A cikin ‘yan kwanakin nan, jami’an tsaro na Najeriya sun yi ta bayar da sanarwa sun a ikirarin kasha ‘yan Boko Haram masu yawa a hare-hare kan tungayensu.

Babu hanyoyin iya tabbatar da gaskiyar wannan ikirarin a saboda an katse hanyoyin sadarwa a akasarin sassan arewa maso gabashin Najeriya, kuma ana zargin rundunar sojojin Najeriya da yin Karin gishiri sosai a kan yawan tsageran da take kashewa, tare da rage yawan sojojinta da aka kasha ko kuma farar hula da suka mutu.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, “a cikin shekarar 2013, an ci gaba da samun Karin damuwa dangane da hali na jinkai a yankin arewa maso gabashin Najeriya, inda aka samu hare-hare har 48 masu alaka da Boko Haram tun lokacin da aka ayyana dokar-ta-baci a yankin.”

Daya daga cikin wadannan munanan hare-hare shi ne wanada aka kai a kan Kolejin Koyon Aikin GHona ta Jihar Yoibe dake Gujba, inda ‘yan bindiga suka shiga cikin makarantar da tsakar dare suka harbe dalibai har 40 dake barci a wannan lokacin.
XS
SM
MD
LG