An Dawo Da Layukan Sadarwa a Wasu Sassan Jihar Yobe

Wani mutum na amfani da wayar hannu.

Wani mazaunin jihar wanda baya so a fadi sunanshi yace "Muna ta murna, gaskiya muna godiya da wannan abu, mun ji dadin dawowar nan, saboda mu muka san irin halin da muka shiga a lokacin rashin layukan waya."
Shaidu sun ce babu sanarwa, sai dai kawai gani suka yi layukan sun dawo misalin sha biyun daren Litinin.

Dawowar layukan sadarwan na zuwa ne kasa da mako daya, bayan da Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Gaidam yayi wa hukumomin tsaro a lokacin da suka kai mishi ziyara gidan gwamnati a Damaturu.

Sai dai har yanzu layukan basu dawo ba a Damaturu, shine ma yasa Muryar Amurka ya kasa jin ta bakin jami’an Gwamnati.

Your browser doesn’t support HTML5

An Dawo Da Layukan Sadarwa A Wasu Wurare A Yobe - 2:44