Accessibility links

Darussan da Majo Hamza Al-Mustapha Ya Koya A Kurkuku

  • Grace Alheri Abdu

Kurkugun da aka daure Al-Mustapha

Majo Hamza Al-Mustapha yace da ana iya biyan kudi, da zai so ya biya domin ganin irin rahamar da Allah ya nuna mashi a lokacin da yake gidan yari.

Majo Hamza Al-Mustapha ya bayyana cewa, ya koyi darussa da dama da ba zai iya koya ba a tsawon rayuwarsa banda a wannan lokacin da aka daure shi. Sabili da haka bisa ga cewarshi, da ana iya biyan kudi, da zai so ya biya domin ganin irin rahamar da Allah ya nuna mashi a lokacin da yake gidan yari. Ya kuma yi addu’a kada Allah ya sa wani yaje fursuna ya dandana irin akuba da aka gasa masu.

A cikin hirarsu da wakilinmu Ladan Ibrahim Ayawa, Al-mustapha yace abu na farko da gwamnati ke bukatar yi na gyara shine tabbatar da adalci da inganta harkokin tsaro.

XS
SM
MD
LG