An Gano Rukodar Jirgin Da Ya Gamu Da Hadari

Jami'ai suna dauke da rukodar jirgin da ya gamu da hadari

Cibiyar bincike haduran jiragen sama ta Najeriya ta bayyana cewa, ta gano rukodar nadar bayanan yadda jirgi yake aiki da aka fi sani da suna “black box"
Jami’ai a Najeriya sun ce mutane akalla 13 sun mutu yau alhamis a lokacin da wani karamin jirgin sama ya fadi jim kadan da tashinsa a Lagos.

Hukumar kula da ayyukan gaggawa ta Najeriya ta ce jirgin ya samu wata matsalar inji ya kuma fado kusa da rumbunan tara mai a bangaren sauka da tashin jiragen sama na cikin gida a filin jirgin Murtala Muhammed dake Ikeja.
Wannan jirgin kamfanin Associated Airlines da aka dauki hayarsa, ya doshi garin Akure ne dake Jihar Ondo.

Akwai mutane 20 a jirgin, cikinsu har da ma’aikatansa. Har ila yau jirgin yana dauke da gawar tsohon gwamnan Jihar Ondo, Olusegun Agagu, wanda za a je binnewa.

Jami’an kula da zirga zirgar jiragen sama na Najeriya sun ce an samu rikoda mai nade bayanan yadda jirgin yake aiki har zuwa lokacin faduwarsa.

Wani mummunan hatsarin jirgin saman da aka yi bara ya sake janyo damuwa game da lafiyar zirga ziorgar jiragen sama a Najeriya. Dukkan mutane 153 dake cikin wani jirgin saman kamfanin dana Airlines sun mutu a watan Yunin 2012, a lokacin da jirgin ya fado kan wasu gidajen jama’a kimanin kilomita 9 kafin ya isa filin jirgin saman na Lagos.