Accessibility links

Sama Da Mutane 100 Sun Mutu A Wani Hadarin Kwale-Kwale

  • Grace Alheri Abdu

Wani jirgin ruwa a ya yi hadari

Wani kwale kwale dauke da mutane da suka je cin kasuwa ya kife a cikin kogin kauyen Malale cikin jihar Naija ya kashe sama da mutane 100

Wani kwale kwale dauke da mutane da suka je cin kasuwa ya kife a cikin kogin kauyen Malale cikin jihar Naija a Najeriya.

Kakakin cibiyar agaji ta gaggawa na jihar Naija , Mohammed Hussain, yace i zuwa maraicen yau asabar, an tsamo gawarwaki 42 na wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hadarin.

Babu labarin ko akwai wadanda suka tsira da rayukansu. Hukumomi kuma basu tabbatar da masababin hadarin ba.

Wadansu mazauna kauyen dai sun ce yana yiwuwa kwale-kwalen ya yi karo da itace ne ya kife, sai dai sakataren gwamnatin jihar Naija, Idris Ndako wanda ya tabbatar da aukuwar hadarin, yace an dauki mutane ne da kaya fiye fiye da yadda ya kamata a jirgin. Bisa ga cewarshi jirgin ya dauki mutane sama da 150 a maimakon mutum 50 da ya kamata a dauka.

A cikin hirarsu da Ibrahim Alfa Ahmed, wakilin Sashen Hausa, Mustapha Nasiru Batsari yace hadarin ya auku ne a wani kauye da ba a iya shiga sai da kwale-kwale. Ya kuma bayyana cewa, mutanen dake kauyukan dake kewaye suna taimakawa wajen nemo gawarwaki.

XS
SM
MD
LG