An Ja Kunnen 'Yan Kungiyar MEND

Shugaban wata kungiyar matasan Arewa yace idan har 'yan yankin Niger Delta suka naiwatar da barazanarsu, to zasu tsokano abinda ba su san iyakarsa ba
Shugaban wata kungiya ta matasan arewacin Najeriya, ya gargadi 'ya'yan kungiyar tsdageran yankin Niger Delta, MEND, da cewa idan suka kuskura suka aiwatar da barazanarsu ta kai farmaki a kan Musulmi, su na iya tsokano abinda ba zasu iya magance shi ba.

A cikin hirar da yayi da Muryar Amurka, malam Aminu Aliyu Kofar Sauri, yace babu wata hujja da 'yan kungiyar ta MEND suke da ita, ta kai farmaki a kan dukkan al'ummar Musulmi dangane da hare-haren da ba a ma tabbatar da ko su wanene suke aikata su a Najeriya da sunan Boko Haram ba.

Ya ce idan har matasan na yankin Niger Delta su na jin cewa su na da matasa 'yan ga-ni-kashe-ni, a arewa ma akwai irin wadannan matasa n, wasu ma wadanda ba a san su ba, balle ma a ce za a ja musu kunne kan kada su maida martani.

A saurari matakai guda uku na gargadin da shugaban matasan na arewa yayi ma 'yan MEND na Niger Delta:

Your browser doesn’t support HTML5

Martani Ga 'Yan MEND Daga Aminu Aliyu Kofar Sauri Katsina