An Kaddamar Da Gidauniyar Marigayi Dan Maraya Jos

Marigayi Alhaji (Dr.) Adamu Dan Maraya Jos

A birnin Jos, an kaddamar da gidauniyar marigayi Alhaji Adamu Dan Maraya Jos, inda aka bayyana kyawawan darusa da wakokin marigayin ke da su, da kuma halayan marigarin.

Anyi kira ga ‘yan Najeriya da su rungumi akidar da zaman lafiya maimakon furta kalaman da ka iya haddasa rikici da rarraba kawunan al’umma.

Mahalarta taron da aka gudanar a Jos, sun bayyana irin kyawawan darussa da wakokin marigayi Alhaji Adamu Dan Maraya Jos, suke yin tasiri wajen inganta zaman takewar al’umma.

Tsohon shugaban gidan Radiyon tarayyar Najeriya, malam Ladan Salihu, ya bayyana marigayi Dan Maraya Jos, a matsayin wanda ya sadaukar da kansa wajen ilimantarwa da hadin kan al’umma da taimakon mabukata da dai sauransu.

Shima shugaban Gidauniyar ta Dan Maraya Jos, Osezua Isibor, ya ce sun kafa gidauniyar bisa la’akari da irin gagarumar gudunmawar da Marigayi Dan Maraya Jos ya bayar ta hanyar wakokinsa wajen gina Najeriya.

Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kaddamar Da Gidauniyar Marigayi Dan Maraya Jos - 3'34"