An Kashe Akalla Farar Hula 7 a Wani Hari a Mozambique

FILE - Residents gather for a meeting in the recently attacked village of Aldeia da Paz outside Macomia, northern Mozambique, Aug. 24, 2019.

An kashe akalla farar hula tara a wani sabon hari da kungiyar tsaurin Islama ta kai a lardin Cabo Delagado mai fama da rikici a arewacin kasar Mozambique, a cewar wasu majiyoyin cikin gida.

Hare haren da aka kai a gundumomin Mocimboa da Praia da kuma Macomia a na Cabo Delgado a ranar Laraba, sun tilasta mutune su arce daga gidajen su, sun kuma suna rabe a wani wurin mai kariya cikin itatuwa, inji mazauna yankin suka fadawa Muryar Amurka.

Mozambican soldiers

Wata kungiyar ‘yan bindiga dauke da kyallaye mai rubutun Islama sun kai sumame a kauyen Tandacua a Macomia, suna neman abinci a cewar mazauna wurin.

Maharan sun isa wurin ne da misalin karfe shida na yamma, agogon kasar, ‘yan kauyen da dama sun arce daga kauyen a cewar wani mazauni kauyen daya nemi a sakaya sunan sa.

Wata kungiyar ‘yan bindiga ta al-Shabab a cikin kasar da aka fi sani da Ahlu Sunna wa Jama ce ta kai wadannan hare-haren a arewacin Mozambique. Ana yi wa wannan kungiyaqr kallon abokiyar kungiyar ‘yan ta’addan IS a Mozambique.