An Kulla Yarjejeniyar Samun Zaman Lafiya Tsakanin Manoma Da Makiyaya a Jihar Plateau

PLATEAU: Sarkin Irigwe Ronku Aka na Bassa da shugabannin Fulani Kirista suka ziyarta

Rundunar wanzar da zaman lafiya a jihar Plateau ta ‘dauki matakin da zai samar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiya a yankin karamar hukumar Bassa.

Cikin ‘yan kwanakin nan rikicin manoma da makiyaya a karamar hukumar Bassa, ya rikide ya koma na kai hari ga juna da ramuwar gayya. A makon da ya gabata an sami asarar rayuka da yawa da salwantar dabbobi da kuma kona gidaje da kayan abinci masu dinbin yawa yayin da jama’a da dama ke gudun hijira.

Shugaban ma’aikatan rundunar wanzar da zaman lafiya a jihar Plateau Birgediya Janar Mohammad Bello, yace sun zauna tare da bangarorin al'umar Irigwe da fulani, inda suka samar da yarjejeniyar zaman lafiya.

Birgediya Mohammad Bello ya kara da cewa duk da cewa shugabannin bangarorin biyu na basu hadin kai ya kamata matasa su kai zuciya nesa.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kula Yarjejeniyar Samun Zaman Lafiya Tsakanin Manoma Da Makiyaya a Jihar Plateau - 3'00"