Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Sabuwa Ta Kunno Kai Tsakanin APC Da PDP A Borno


PDP
PDP

An shiga wani sabon rikici tsakanin ‘yan jam’iyar APC mai mulki da kuma babban jam’iyar adawa PDP a jihar Borno kan mallakar wani gini da ake kira Premier Cinema a matsayin ofishin siyasa.

Wannan gini dai ya dade a hannun jam’iyun siyasa dabam dabam, wanda daga bisani jam’iyar APC mai mulki ta karbi hayar ginin a matsayin ofishinta har na tsawon lokaci kafin daga baya jam’iyar PDP tace ofishinta ne ta kuma shiga canzawa ginin fenti.

Ana cikin aikin canza fentin zuwa kalar jam’iyar PDP jami’an tsaro suka dakatar da aikin, daga bisani kuma gwamnatin jam’iyar APC tasa buldoza ta rusa ginin da sunan cewa, ta biya kudin ginin kuma ta rusa shi da niyar gina makarantar islamiya.

Jam’iyar PDP tace ta riga ta kama haya a ginin kuma jama’iyar APC tayi aiki da karfin mulki ne ta ruguza ginin zarginda jam’iyar APC ta musanta.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda Bi’u ya aiko mana daga Maiguguri.

Rikicin APC da PDP a Borno-3:26"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG