Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddama Kan Sahihancin 'Ya'yan Hamma Ahmadu


Jagoran 'yan adawar Nijar Hamma Ahmadu

Bullar wata shu'umar wasika wacce ake danganta ta da gwamnatin Najeriya ta dada yamutsa fagen siyasar Janhuriyar Nijar ganin wannan takarda na ikirarin cewa Ma'aikatar Shari'ar Najeriya na bukatar a tabbatar da sahihancin 'yan'yan madugun 'yan adawar Nijar, Hamma Ahmadu.

Takaddamar da aka dade ana yi kan sahihancin ‘ya’yan jagoran ‘yan adawar Janhuriyar Nijar Hamma Ahmadu ta dau wani sabon salo. Wannan kuwa ya biyo bayan bullar wata wasikar da aka ce ta fito ne daga Ma’aikatar Shari’ar Tarayyar Najeriya zuwa Ofishin Jakadancin Najeriya a Janhuriyar Nijar dauke da bukatar a gwada kwayar halitta (ko “DNA”) ta matar Hamma Ahmadu mai suna Hadiza Hamma Ahmadu don a tantance sahihancin kasancewar wata yarinya mai suna Fadima Lilian Ahmadu da wani yaro mai suna Ahmadu Guellan ‘ya’yan matar Hamma Ahmadu mai suna Hadiza Hama Ahmadu ne ko a’a.

To saidai lauyan da ke kare matar Hamma Ahmadu din wato Ali Kadiri na ganin wannan ba wani abu ba ne illa wata makarkashiyar sisaya saboda abin mamaki ne a ce gwamnatin Najeriya ta tsoma kanta cikin rigimar siyasar Janhruiyra Nijar. Malam Kadiri ya ce wani abin da ya kara kawo shakku kan sahihancin wasikar shi ne yadda aka yi wasikar da ya kamata a ce ta sirri ce ta wanzu tsakanin jama’a. Don haka, in ji Kadiri, sun a ganin wannan wasikar wasu mahassada ne kawai su ka kirkiro ta su ka wanzar da ita tsakanin ‘yan Nijar don kawai su tozarta iyalan Hamma Ahmadu.

Wakilinmu a Yamai Sule Mummuni Barma ya yi yinkurin jin matsayin hukumomi a Janhuriyra Nijar game da wasikar to amma babu wanda ya yadda ya masa bayani a gwamnatance. To sai dai wani babban kusa a jam’iyyar PNDS mai mulki ya ce shi ya yi imanin cewa wannan wasikar daga hukumomin Najeriya ta fito saboda a baya jami’an gwamnatin Najeriya sun zo kan wannan batun. Ya ce yanzu haka yaran na hannun hukumomin Najeriya.

Ga dai wakilinmu a Yamai Sule Barma da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG