An Sace ‘Yan Sandan Kasa da Kasa

Rundunar kare zaman lafiya ta hadin gwiwar MDD da Tarayyar Afirka, UNMID, ta bada sanarwar sace jami’an ‘yan sandanta biyu ran Asabar da safe a Nyala, cibiyar yankin kudancin Darfur-kasar Sudan.

MDD tayi yekuwar cewa an sace jami’anta biyu, masu ayyukan badashawara ga ‘yan sandan kasa da kasa dake aiki a rundunar hadin gwiwar kare zaman lafiya ta MDD da tarayyar Afirka dake yankin Darfur.

Rundunar hadin gwiwa ta ayyukan kare zaman lafiya, UNMID, tace a ran Asabar da safe ne a Nyala, cibiyar yankin kudancin Sudan dake Darfur, wasu katti uku a cikin mota suka kame jami’an na MDD bayan sun fito daga masaukinsu kan hanyarsu ta zuwa sansanin sojin hadin gwiwa, bayan sun yi barazanar harbesu da bindiga sannan suka cusasu a mota suka tsere dasu. MDD tace zata gudanar da cikakken bincike.