Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka ya Amince da Ginin Masallachi


Shugaban Amurka ya Amince da Ginin Masallachi

Shugaban Amurka Barack Obama ya jaddada amincewarsa da furcin da yayi na cewa Musulmi nada ‘yancin gina wajen ibadarsu a birnin New York.

Shugaban Amurka Barack Obama ya jaddada goyon bayan da yake baiwa ‘yancin da Musulmin Amurka ke dashi na gina Masallachi a kusa da inda aka kai hare-haren ta’addancin sha daya ga watan Satumban shekarar 2001 a birnin New York. Idan an tuna, a lokacin gaisuwar bude baki da shugabannin Musulmin Amurka suka kai fadar shugaban Amurka ta “White House”, ran Juma’a shugaba barack Obama bayan yin maraba lale da zuwan watan Azumin watan Ramadan yake cewa Musulmi nada ‘yancin gina wajen ibadarsu a yankin Manhattan. Yace Amurka an ginata ne bisa tuwasun ‘yanci da walwala.

XS
SM
MD
LG