Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Afirka Ta Kudu Sun Kawo Karshen Neman Karin Gawarwaki


'Yan Sandan Afirka Ta Kudu Sun Kawo Karshen Neman Karin Gawarwaki

Bayan da aka gano gawarwaki hudu alhamis a cikin ramin hakar ma'adinai, 'yan sanda sun shiga domin neman ko akwai karin gawarwaki ko mutanen dake da rai a ciki.

'Yan sandan Afirka ta Kudu sun kawo karshen binciken da suka gudanar cikin wani ramin hakar ma'adinai da aka daina amfani da shi, inda a jiya alhamis aka gano gawarwaki hudu.

'Yan sandan sun fada yau Jumma'a cewa har yanzu su na binciken yadda aka yi wadannan mutane hudu suka mutu. Amma sun ce ba a samu karin gawa ba a lokacin da suka karade cikin ramin hakar ma'adinan da safiyar Jumma'ar nan.

Kamfanin hakar ma'adinai mai suna Aurora ya tabbatar da cewa masu gadinsa sun yi musanyar wuta ranar litinin da masu satar hakar ma'adinai a ramin hakar ma'adinan na Grootvlei, mallakar Khulubuse Zuma, dangin shugaba Jacob Zuma da kuma wani jikan tsohon shugaba Nelson Mandela mai suna Zondwa Mandela.

Amma a lokacin da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Afirka ta Kudu, wani jami'in kamfanin, Thulani Ngubane, ya kare masu gadi na kamfanin. Ya ce a can baya, masu satar hakar ma'adinai su na kai farmaki a kan masu gadin, kuma hakkin masu gadin ne su kare kadarorin da aka damka musu amanar tsarewa.

Kungiyar Ma'aikatan Hakar Ma'adinai ta Kasa ta Afirka ta Kudu ta yi kiran da a gudanar da bincike, tana mai fadin cewa watakila gawarwakin da aka samu na ma'aikatan wannan kamfani ne wadanda aka yi wata da watanni ba a biya su albashi ba, suka kuma rasa na yi a lokacin da aka rufe wannan mahaka.

Jam'iyyar ANC ta shugaba Zuma ta yi tur da mace-macen. Jam'iyyar ta ce ai kamata yayi masu gadin kamfanin su kira 'yan sanda idan har sun yi imani da cewa ana aikata wani laifi a wurin, maimakon yin musanyar wuta da mutanen.

XS
SM
MD
LG