An Sake Gano Wani Shirin Kai Hari A Birnin Paris

Boussy-Saint-Antoine

‘Yan Sanda a Faransa sun tarwatsa wata makarkashiyar kai wani mummunan harin ta’addanci a birnin Paris a kwanaki biyu da suka gabata, inda suka kame wani matashi mai shekaru 15, da ake zarginsa da shirya harin ta’addanci.

Kame yaron da akayi ranar Asabar yazo ne kwanaki biyu bayan da ‘yan sanda suka ce sun kame wasu ‘yan mata dake kokarin kai hari a Majami’ar Notre Dame da wasu gurare.

Jami'ai masu binciken sirri sun zargi yaron da cewa yana shirin kai hari da kuka a wani wajen haduwar jama’a, amma jami’an sunki bayyana sunan gurin da yake shirin kai harin.

Labarin kama yaron ya zone jim kadan bayan da Fara Minista Manuel Valls, yace a jiya Lahadi, kusan mutane 15,000 a Faransa ake bin sawunsu saboda ana zargin cewa ana cikin juyar musu da tunaninsu zuwa tsatstsauran ra’ayi, haka kuma wasu 1,350 ana bincikarsu, daga ciki harda 293 da ake tuhumar suna da alaka da wata kungiyar ta’addanci.

Faransa dai tana cikin dokar ta baci bayan da aka kai mata hare hare har sau uku cikin shekarar nan, ciki harda harin da aka kai da katuwar mota a garin Nice wanda ya kashe mutane 86. Wanda ya biyo wasu hare hare biyu da aka kai a shekarar da ta gabata da suka hada da na ranar 13 ga watan Nuwamba a kan gidajen cin da mashayun barasa da kuma wani filin wasa, wadanda a hade aka hallaka mutane 130 a cikinsu.