An Sake Sakin Wasu Karin Dalibai Da Aka Sace a Birnin Yauri

Ranar Asabar wani rukuni na daliban da aka sace a makarantar Sakandaren birnin Yauri ta jihar Kebbi ya iso a fadar gwamnatin jihar.

Rukunin wanda ya kunshi dalibai talatin da malami daya, gwamnan jihar Abubakar Atiku Bagudu ne ya karbe su a fadar gwamnatin, bayan kwashe fiye da kwanaki 200 a hannun 'yan bindiga.

Gwamnatin ta ce za a duba lafiyar yaran kafin a mika su ga iyayen su.

Wani bayani da mashawarcin gwamnan jihar Kebbi da daren ranar Asabar, ya bayyana godiyar gwamnati ga jami'an tsaro da duk wadanda suka taimaka ga ceto yaran da kuma shugaban kasa Muhammad Buhari akan wannan nasarar da aka samu.

A wata zantawa da wasu daga cikin iyayen yaran da aka sace, sun ce kawo yanzu ba a sanar da su dawowar yaran ba a hukumance, amma dai tuni suna a garin na Birnin kebbi,suna dakon kira daga gwamnatin.

Idan ba a manta ba dai ranar 17 ga watan Yuni na shekara ta 2021 ne aka sace yaran a makarantar su dake garin Birnin Yauri, a karamar hukumar Ngaski ta jihar kebbi, inda ranar alhamis 21 ga watan Oktoba 2021 aka ceto yara da malamai da adadinsu ya kai 30, har yanzu akwai ragowar yaran dake hannun 'yan ta'addar.