An Sake Tuhumar Omoyele Sowore, Da Hada Taro Ba Bisa Ka'ida Ba

Kotu ta sake tura Omoyele Sowore, gidan jiran hukunci, akan zargin shi na tada zaune tsaye.

Wata Kotun majistare a Abuja ta tura dan jaridar nan kuma dan rajin tabbatar da demokaradiyya, Omoyele Sowore, ma'adana a gidan yarin Kuje gabanin duba bukatar ba da belin sa.

Sowore wanda shi ne mawallafin jaridar yanar gizo ta Sahara Reporters, kazalika ya jagoranci zanga-zangar juyin juya hali da 'yan sanda su ka zarge shi da yunkurin kifar da gwamnati ko cin amanar kasa.

Wannan karo 'yan sanda sun kama Sowore da gurfanar da shi gaban kotu don zarginsa da tada fitina da gudanar da haramtaccen taro.

"Wani ya na kiran a sauya gwamnati da halin makarkashiya, ba tare da bin tanadin tsarin mulki ba" inji lauyan bangaren shigar da kara James Idachaba.

Lauyan Sowore mai suna Marshal Abubakar ya ce, Sowore ya shiga kare masu zanga-zanga yayin da ya ga a na dukan daya daga cikinsu a yankin Gudu da ke Abuja.

"A lokacin da Sowore ya ke sa baki don dakatar da cin zarafin mutumin, sai jami'ar 'yan sanda DSP Altine Daniel, ta yi dirar mikiya a kan sa har da fasa ma sa hanci." Inji Marshal Abubakar.

Lauyan ya cigaba da cewa an kai su Sowore ofishin jami'an SARS da a ka soke a ka cigaba da azabtar da su.

Sowore, ya zargi gwamnatin Buhari da cin zalin sa ya na mai cewa ya gano ma har yanzu ba a rushe rundunar SARS ba.

"Lokacin da a ka kai mu ofishin tsare mutane na Abatuwa, na gano gwamnati ba ta rushe SARS ba, don sun tattaro 'yan SARS su ka doke mu da tura mu dakin tsare mutane."

Alkalin kotun Mabel Segun Bello ya tsayar da Talatar nan don duba neman belin Sowore.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya a cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

An Sake Tuhumar Omoyele Sowore, Da Hada Taro Ba Bisa Ka'ida Ba

Karin bayani akan: Najeriya​, SARS, Omoyele Sowore, da Nigeria.