Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miyagu Sun Fara Gajiya Da Kauyuka a Arewacin Najeriya


Shugaban Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu
Shugaban Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu

Lamarin tsaro na ci gaba da zama wa Najeriya kadangaren bakin tulu, domin ayyukan ta'addanci sun fara gurgusowa daga kauyuka zuwa cikin birane, tamkar yadda ya faru cikin garin Sakkwato, inda mahara dauke da bindigogi suka yi dirar mikiya a unguwar Gidan Igwai.

A can baya ayukkan ta'addanci suna faruwa ne akasari a yankunan karkara, inda ake da karancin jami'an tsaro da kayan aiki, amma yanzu labarin ya fara canjawa.

Unguwar Gidan Igwai dake gefen birnin Sakkwato ta kan hanyar zuwa jami'ar Usmanu Danfodiyo, ta dauki bakuncin bakin da ba a bukatar zuwansu, inda suka kai farmaki a wasu gidaje da shaguna tare da harbi da kuma karbar kudaden jama'a.

Alhaji Sule Yakubu dan kasuwa ne da yake cikin wadanda ‘yan bindigar suka kai wa farmaki, inda suka dauki tsawon lokaci a gidansa su na ta bala'i.

Ya ce sun shiga gidansa da muggan makamai kamar bindigar AK47 da sauransu, kana suka bukaci Naira miliyan goma ko kuma su kashe shi. A cewar Alhaji Sule, bayan sun karbi wasu ‘yan kudade a hanunsa sun tafi ba tare da taba lafiyarsa ba.

Bayan fitowarsu daga gidan Alhaji Sule, barayin sun yi ma wani shago ruwan albarusai suka dauki kayayyaki har ma sun harbi mai tsaron shagon ya samu kariya biyu a kafa.

A garin Tangaza ma ‘yan bindiga sun kai farmaki wani kauye da ake kira Tukkandu, inda suka harbi mutum biyar kuma suka yi garkuwa da mutum daya kamar yadda wani Yusuf Hussaini ya bayyana.

Duk wadannan suna faruwa ne lokacin da jami'an ‘yan sandan al'umma suke shirin fara aiki bayan kammala karbar horo a makon jiya.

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Sakkwato Ibrahim sani ka'o'je yace an baiwa jami'an horo ta yadda zasu iya aikin samar da tsaro.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne irin tasirin da aikin jami'an na ‘yan sandan al'umma zai yi daidai lokacin da ‘yan bindiga ke dada maida hankali kan birane suna sa al'umma kokawa.

Ga dai cikakken rahoton Muhammad Baisr daga Sokoto:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Karin bayani akan: sojojin Najeriya​, sojoji, Muhammad Adamu​, da Nigeria.

XS
SM
MD
LG