An Samu Karuwar Mace-mace A Jihar Yobe

Rahotanni daga jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya na nuna cewa an samu karuwar mace-mace a jihar a cikin 'yan kwanakin nan, ko da yake hukumomin kiwon lafiya ba su tabbatar da sanadiyyar mace-macen ba. A halin yanzu dai lamarin ya jefa al'ummar jihar cikin damuwa.

Usman Bin Affan, dan jihar Yobe ne, ya ce galibi dattawa ne ke mutuwa a jihar, musamman garuruwan Potiskum, da Bade har ma Damaturu.

Wani mai kula da makabarta a garin Potiskum ya ce a cikin kwana biyu sun binne kusan mutum 40, ko a ranar Alhamis 7 ga watan Mayu ya ce sun binne mutum 14 shi ya sa suka sanar da hukumomi halin da ake ciki.

Dr. Mohammed Lawal Gana, kwamishinan lafiyar jihar, ya ce a hukumance babu wata shaida da ta nuna cewa mace-macen da ake yi yanzu sun fi na baya, tunda ba a gudanar da wani bincike ba kuma akan samu mace-mace a lokacin zafi. Ya kuma ce ba lallai ba ne mace-macen na da alaka da cutar coronavirus.

Ga karin bayani cikin sauti daga Hassan Maina Kaina:

Your browser doesn’t support HTML5

An Samu Karuwar Mace-mace A Jihar Yobe