An Yi Kira Ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Karfafa Kananan Asibitocin Kiwon Lafiya

Wasu mata da yara suna jiran ganin likita a karamin asibiti

Kungiyar likitocin kula da lafiyar iyali ta duniya (WONCA) ta yi kira ga Gwamnatin tarayyar Najeriya ta karfafa kananan asibitocin kiwon lafiya (PHC), domin wannan zai rage kudaden da gwamnati ke kashewa a kan kiwon lafiya
Kungiyar likitocin kula da lafiyar iyali ta duniya (WONCA) ta yi kira ga Gwamnatin tarayyar Najeriya ta karfafa kananan asibitocin kiwon lafiya (PHC), domin wannan zai rage kudaden da gwamnati ke kashewa a kan kiwon lafiya.

Bisaga shugaban kungiyar na sashin Africa Dr. Sylvester Osinowo, yace, kananan asibitocin kiwon lafiya zasu taimaka wajen rage kudaden da gwamnati ke kashewa a kan kiwon lafiya. Dr. Osinowo ya yi wannan kiran ne a lokacin taron kungiyar a legos, wanda ke da take: magani domin iyali: shawara da karfafa kananan wuraren kiwon lafiya a sashin Africa.

Ya kara da cewa, wannan zai rage kashe kudi, ya kare jama’a daga kamuwa da wadansu cututuka ya kuma zama da taimako ga jama’a domin yana kusa da kauyukan su.

Shugaban kungiyar likitocin na shiyar Afrika ya bayyana cewa, kungiyar likitocin da kuma kungiyar lafiya ta duniya sun kakkafa kananan dakunan kiwon lafiya masu aiki a kasashe da yawa, ya kara bayyyana dalilin da yasa kungiyar ta zabi taken wannan shekara, domin ta wayar da kan gwamnati da sauran kungiyoyi akan bukatar kafa irin wadannan kananan wuraren kiwon lafiya.