An Yi Nasarar Gwajin Magungunan Ebola

Gwajin Maganin Ebola

Rubu’i biyu na magungunan cutar Ebola da aka gwada a Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo, sun yi matukar inganci ta yadda ma za a fara bai wa masu fama da cutar ta Ebola.

Nasarar magungunan biyu, wadanda aka fi sani da REGN-EB3 da mAb-114, sun sa masu ilimin kimiyya sun yanke shawarar tsai da binciken da ake yi kansu, a maimakon haka su na son a maida hankali kan yadda za a fara amfani da su a Afirka, inda annobar cutar ta tsawon shekara guda ta lakume rayuka sama da 1,800

“Daga yanzu, ba za a kara cewa Ebola ba ta warkuwa ba,” abin da Jean-Jacques Muyembe, daraktan Cibiyar Binciken Cututtuka ta Kasar Congo, ya gaya ma jaridar The Guardian kenan. Ya kara da cewa, “Wannan cigaban da aka samu zai taimaka wajen ceto dubban rayuka.”