An Yi wa Pele Tiyata a Hanji

Tsohon dan wasan Brazil Pele

Dan shekara 80, Pele, shi ne dan wasan kwallon kafa namiji da ya taba lashe kofin duniya sau uku.

An yi wa fitaccen tsohon dan wasan kwallon kafa na Brazil Pele aiki a asibiti inda aka cire masa wani kumburi a jikin hanjinsa.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito cewa asibitin Albert Einstein da aka yi wa Pele aiki a Sao Paulo ya tabbatar da yi wa dan wasan aiki.

Pele ya shiga shafinsa na sada zumunta a ranar Litinin ya ce “an yi nasara a aikin.”

“A ranar Asabar na je aka yi min tiyata aka cire min wani kumburi a jikin hanjina, an gano shi ne a lokacin da na je duba lafiyata.” Pele ya ce.

“Na godewa Allah da samun sauki da kuma Dakta Fabio da Dr. Miguel wadanda suka kula da lafiyata.”

Dan shekara 80, Pele, shi ne dan wasan kwallon kafa namiji da ya taba lashe kofin duniya sau uku.

Ya samu larurar tafiya tun bayan da aka yi masa wani aiki a saman cinyarsa a shekarar 2012.

Hakan ya sa ya zama dole sai da taimakon abin dogarawa ko kujera yake shiga jama’a.

An kuma taba kwantar da shi a asibiti a ‘yan shekarun baya saboda matsalar koda da ya fuskanta.

Brazil ta lashe kofin duniya a shekarun 1958, 1962 da kuma 1970.

Pele shi ne dan wasan da ya fi ci wa kasar ta Brazil yawan kwallaye inda yake da 77 a wasa 92 da ya buga mata.