Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mece Ce Makomar Juventus Bayan Tafiyar Ronaldo?


Dan Wasan Juventus Federico Chiesa

Har yanzu Juve ba ta lashe wasa ko daya a wannan sabuwar kakar wasanni ba yayin da ta buga guda biyu.

Juventus ta sha kaye a gida a hannun Empoli da ci 1-0 a gasar Serie A, Wasan da ta buga a karon farko ba tare da Cristiono Ronaldo ba.

Ronaldo na shirin komawa tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United a gasar Premier ta Ingila, wacce ya baro shekara 12 da suka gabata.

Dan wasan Empoli Leonardo Mancuso ne ya zura kwallo a ragar Juventus a ranar Asabar, lamarin da ya zo a matsayin abin mamaki ga mutane da dama.

A kwanan nan aka daga darajar kungiyar ta Empoli ta shiga gasar ta Serie A a matsayin sabuwar kungiya.

Da yawa kuma sun yi zaton Juventus za ta yi kaca-kaca da su amma sai kungiyar ta shammaci Juventus.

Rashin tabuka komai da ‘yan wasan Massimiliano Allegri yi, ya fusata magoya bayan kungiyar ta Juventus a karshen wasa.

Har yanzu Juve ba ta lashe wasa ko daya a wannan sabuwar kakar wasanni ba yayin da ta buga guda biyu.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG