Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ronaldo Ya Ceci Portugal A Hannun Ireland


Cristiano Ronaldo a lokacin da ya ci kwallo ta biyu
Cristiano Ronaldo a lokacin da ya ci kwallo ta biyu

Sakamakon wasan ya ba Ronaldo dan shekara 36 damar wuce Daei wanda ya zura kwallaye 109 cikin wasanni 148 da ya bugawa kasarsa ta Iran.

Cristiano Ronaldo ya zura kwallaye biyu a mintinan karshe a wasan da kasarsa ta Portugal ta buga da kasar Ireland a karawar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.

Kwallayensa sun sa an tashi a wasan da ci 2-1, nasarar da har ila yau ta ba shi dama ya kawar da tarihin tsohon dan wasan Iran Ali Daei da ya fi cin kwallaye ga kasarsa.

Ronaldo ya zura kwallon farko ne a minti na 89 yayin da Ireland take gaba a wasan da ci 1-0.

Kwallon ita ce ta 110 da ya ci wa kasarsa a wasanni 180 da ya bugawa Portugal.

Ronaldo yana murnar cin kwallo ta biyu
Ronaldo yana murnar cin kwallo ta biyu

Jim kadan bayan kwallonsa ta farko wacce ta kai wasan 1-1, Ronaldo ya kuma zura wata kwallon cikin mintinan da aka kara, abin da ya kai wasan 2-1 ya kuma ba Portugal nasara a karshe.

Sakamakon wasan ya ba Ronaldo dan shekara 36 damar wuce Daei wanda ya zura kwallaye 109 cikin wasanni 148 da ya bugawa kasars ta Iran.

Daei tsohon fitacce dan wasan kasar Iran ne da ya shahara a tsakanin shekarun 1993-2006 wanda mafi aksarin rayuwar kwallonsa ya yi ta ne a nahiyar Asiya.

Ko da yake, ya dan taka leda na dan kankanin lokaci a gasar Bundesliga ta kasar Jamus.

A farkon makon nan Ronaldo ya yi kome zuwa tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United bayan da ya baro Juventus a Italiya.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG