Ana Ci Gaba Da Shirye-Shiryen Ganawar Shugaban Amurka Da Na Koriya Ta Arewa

Trump Da Kim

Wakilan Amurka da na Koriya ta Arewa sun yi taro jiya Lahadi 28 ga watan Mayu a kebantaccen yankinnan da ya raba ita Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu don kamalla shirye-shiryen taron kolin da ake sa ran zai faru a tsakanin shugaba Donald Trump da shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un.

Bayan da ya soke taron a ranar Alamis da ta wuce, shugaba Trump ya dawo yace har yanzu maganar yin taron tana nan kamar yadda aka shirya ta tun farko, ran 12 ga watan gobe na Yuni a Singapore.

Jakadan Amurka a kasar Philippines wanda kuma ya taba zama jakadanta a Koriya ta Kudu, Sung Kim, shine yake jagorantar wakilan Amurka a wajen taron share fagen taron kolin, kuma ana jin za a kai gobe Talata ana tattaunawar.

Har zuwa yanzu dai ba tabbas na dalilan da suka sa Trump ya sauya ra’ayinsa game da soke taron ba, kwana daya bayan ya bayyana cewa ya kagara ya gana da shugaban na Kiriya ta Arewa.

Amma dai an san cewa Trump ya fusata da zagin da wasu jami’an Koriya ta Arewan suka yi wa mataimakinsa, Mike Pence, bayan da shi Pence din ya bayyana ra’ayin cewa Koriya ta Arewa za ta karkare kamar Libya, wadda bayan ta saki makamanta, aka zo aka yi kaca-kaca da ita, har aka kashe shugabanta, Muammar Gadhafi.